ABNA24 : Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto Muhammad Baqir Muhammadi shugaban asibitin yana fadar haka a jiya Jumma’a. Muhammadi ya kara da cewa asibintin ya na karban mutane daga ko wace kasa suka fito, sannan asibitin ya na da sassa da dama, wadanda suka hana da bangaren tiyata, da cututtukan kashi, yara, kwanya, da jijiyoyi da sauransu.
Muhammadi ya ce ya zuwa yanzu sun gudanar da ayyukan tiyata wa mutane 10 daga cikin har da hada jijiyoyin da suka tsinke sandiyar tashin bom na ranar 4n ga wata. Banda haka sun fitar da karafa da wasu abubuwa da suka shiga jikin mutane da dama.
A ranar 4 ga watan Augustan da muke ciki ne wasu fashe-fashe a tashar jiragen ruwa na Beirut suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 177 a yayinda wasu kimani 7000 suka ji rauni.
342/